IQNA

21:54 - July 01, 2016
Lambar Labari: 3480570
Bangaren kasa da kasa, Babbar cibiyar Musulmi a kasar Amurka ta bayyana cewa, jahar Florida ta zama wata babbar matattarar masu tsananin adawa da muslunci.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin watsa labarai na Orlando Sentinel cewa, babbar cibiyar cibiyar mabiya addinin muslunci ta kasar Amurka CAIR ta fitar da bayani da ke cewa, jahar Florida ita ce jahar da aka fi nuna tsananin kyama da adawa ga musulmi a tsakanin dukkanin jahohin kasar Amurka, inda ake samun karuwar hare-hare kan musulmi da cibiyoyinsu.

Rasha Mubarak tana daga cikin masu kula da harkokin cibiyoyin musulmia wanann jaha ta bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun baya-bayan nan an samu hare-hare a kan cibiyoyin musulmi da masallatansu da dama a cikin wannan jaha, kamar yadda kuma cin zarafi a kan daidaikun musulmi mazauna wannan jaha yake kara ta'azzara.

Bayanin cibiyar muuslmin ta vAmurka CAIR ya kara da cewa, sakamakon kamfe da dan takarar shugabancin kasar Amurka Donald Trump ke yi na kyamar musulmi, hakan ya kara ruruta wutar kyamar musulmia wannan jaha a baya-bayan nan.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa akwai wasu kungiyoyi 33 a kasar masu adawa da musulmi, 3 daga cikinsu suna da mazaunin a jahar Florida, wanda hakan ya sanya cibiyar musulmin ta CAIR yin kira ga mahukunta musamman a wannan jaha da su dauki matakan da suka dace domin kare rayukan musulmi da dukiyoyinsu da kuma wuraren ibadarsu, kamar yadda dokar kasar ta tanada.

3511386

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: