IQNA

An Kame Mutanen Da Ake Zargi Da Hannu A Harin Madina Da Qatif / Mutane 19

23:29 - July 08, 2016
Lambar Labari: 3480591
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin cikin gida akasar saudiyya ta ce an kame mutane da ake zarginsu da kame mutanen da ke da hannua harin Madina d kuma Qatif su 19 da ‘yan Pakistan 12.

Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na kafanin dillancin labaran Reuters cewa, kakakin ma’aikatar harkokin cikin Saudiyya Mansur Turki ya ce sun kame wasu mutane kan zarginsu da hannu a harin ta’addanci.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Saudiyya ta sanar da kame 'yan ta'adda 19 ne da suke da hannu a hare-haren baya-bayan nan da aka kai a cikin kasar musamman harin kunan bakin wake a harabar Masallacin fiyayyen halitta Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w}.

A bayanin da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Saudiyya ta fitar a yammacin jiya Alhamis ya fayyace cewa: 'Yan ta'addan 19 da aka kama suna da hannu a shirya kai hare-haren ta'addanci a Masallacin Manzon Allah Muhammadu dan Abdullahi {s.a.w} da kuma garin Qatif da ke yankin gabashin kasar. Daga cikin 'yan ta'addan 19, bakwai daga cikinsu 'yan asalin kasar ta Saudiyya ne, yayin da 12 'yan kasar Pakistan ne.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Saudiyya ta fayyace cewa: Dan ta'addan da ya tarwatsa kansa a harabar Masallacin Manzon Allah {s.a.w} mai suna Na'ir al-Nujiaidi al-Balawi dan shekaru 26 a duniya dan kasar ta Saudiyya ne kuma kafin shigarsa cikin gungun 'yan ta'adda ya shahara da shaye-shayen muggan kwayoyi.

Bayanin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Saudiyya ya kara da cewa: 'Yan ta'adda uku da suka kai harin kunan bakin wake a Masallacin 'yan shi'a a garin Qatif da ke yankin gabashin kasar a ranar Litinin da ta gabata sune Abdul-Rahman Saleh Muhammad da Ibrahim Saleh Muhammad da kuma Abdul-Karim al-Hesni dukkaninsu 'yan asalin kasar ta Saudiyya ce.

3513431

captcha