IQNA

23:34 - July 15, 2016
Lambar Labari: 3480612
Bangaren kasa da kasa, babban injiniya mai kula da ayyukan gini a hubbaren Imam Hussain (AS) ya bayyana ci gaba da tsayuwar gishikan hubbare a matsayin wata mu’ujiza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hulda da jama’a a hubbaren Husaini cewa, Ali Muhajiri babban injiniya mai kula da ayyukan gini a hubbaren Imam Hussain (AS) ya sheda cewa bisa la’akari da jimawar gishikai na hubbare wadanda na katako har zuwa wannan lokaci da babban abin mamaki.

Ya kara da cewa wannan gishikai suna dauke da gini mai nauyin ton 1200, kuma lokacin da ya kamata a canja su ya wuce, kuma har yanzu babu abin da ya faru, y ace ko shkaka bababu a mahanga ta ilimin gini wannan babbar mu’ujiza ce daga ubangiji.

Haka nan kuma ya ishara da cewa a cikin wannan yanayin injiniyoyi suna ci gaba da yin aiki domin ganin an canja wadannan gishikai da suk dauke da gini mai nauyin ton 1200 a wannan hubbare mai tsarki na Imam Hussain (AS) kuma da yardarm Allah za a kamala aiki a cikin kankanin lokaci.

Ya ce yanzu haka dai an kamala kimanin kasha 25 cikin dari na aikin da ake yin a kara karfin gishikan da ke dauke da ginin wannan hubbare mai tsarki.

3515099

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: