IQNA

23:44 - July 17, 2016
Lambar Labari: 3480618
Bangaren kasa da kasa, Masarautar mulkin mulukiya ta kasar Bahrain na shirin gurfanar da Ayatollah Sheikh Isa Kasim a gaban kuliya bisa zarginsa da karbar kudaden zakka da khumusi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin tashar talabijin ta alalam ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da babbar kotun masarautar mulkin mulukiya ta iyalan gidan khalifa da ke rike da madafun iko a Bahrain ta bayar ta bayyana cewa, a cikin wata mai kamawa za ta gurfanar da wani malami a kasar wanda yake karbar zakka ba da izinin gwamnati ba.

Wannan sanarwa dai tana yin ishara ne kai tsaye ga Ayatollah Sheikh Isa Kasim babban malamin addini a kasar, wanda kuma mafi yawan al'ummar kasar suna daukarsa a matsayin shugabansu na addini.

Tun a cikin watan azumi da ya gabata ne dai masarautar kasar Bahrain ta sanar da cewa ta janye masa izinin zama dan kasa, bisa hujjar cewa yana goyon bayan masu adawa da masarautar, tare da karbar zakka da khumusi ba tare da izinin gwamnati ba.

Tun daga lokacin da masarautar ta sanar da hakan har yanzu kasar ana cikin zaman zullumi, yayin dubban mutane daga ko'ina cikin kasar suka tare a garin Diraz mahaifar Ayatollah Isa Kasim inda kuma a nan yake da zama, sauran mutane a sassan kasar kuma suna cikin shirin fuskantar kowane irin mataki da mahukuntan kasar ka iya dauka a babban malamin.

A nasu bangaren majalisar dinkin duniya da kungiyar tarayyar turai da sauran kungiyoyi na kare hakkin bil adama da suka hada dakungiyar afuwa da human rights watch da sauransu sunyi kakkausar suka dangane da wannan mataki na masarautar Bahrain, tare da yin kira ga masarautar da ta gaggauta janye wannan mataki da ta dauka na siyasa da nuna bambancin mazhaba a kan mabiya mazhabar shi'a, wadanda su ne fiye da kashi tamanin na al'ummar kasar baki daya.

3515648

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: