IQNA

23:41 - July 18, 2016
Lambar Labari: 3480624
Bangaren kasa da kasa, Al'ummar kasar Bahrain a dukkanin yankunan kasar sun fito akn tituna suna nuna rashin amincewarsu da hukuncin da kotun masarutar kasar ta yanke na rusa babbar jam'iyyar siysa a kasar ta Alwifaq.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin Daily Star cewa, al'ummar kasar Bahrain sun fito a kan tituna na yankunan kasar domin yin Allawadai da kuma nuna rashina mincewarsu da wanann mataki da suke bayyana shi da cewa na fir'ananci ne, jami'an 'yan sanda sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu jerin gwanon.

Akasarin al'ummar kasar Bahrain wadanda mabiya mazhabar shi'a ne, suna goyon bayan wannan jam'iyya, wadda masarautar kasar ke kallonta a matsayin barazana gare ta a siyasance, bisa la'akari da abin da ya farua cikin shekara ta 2001, inda aka gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar a karon farko, kuma wannan jam'iyya ta lashe zaben, wanda hakan ya sa sarkin kasar ya rusa majalisar, ya nada wasu 'yan majalisa da yake bukata.

Wannan mataki dai yana ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga bangarorin daban-daban na duniya.

3515683

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: