
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Peninsula cewa, an raba kimanin kwafi dubu 120 a Saliyo, sai kuma Philipines dubu 80 da Nijar dubu 80.
An buga kwafin kur’anan ne a cikin harsunan dubiya daban-daban, turancin Ingilishi dubu 25, Faransanci dubu 25, Spaniyanci dubu 22 Swahili dubu 22, sai kuma Chinese dubu 5, Philipinanci kwafi dubu 21, an kuma raba su ga kasashe 50 masu bukata.
Watan cibiya ce dai take daukar nauyin gudanar da wanann aiki a kasar Qatar wadda take da alaka da ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar, ind ake bayar da makdan kudade domin gudanar da wannan aiki.
An dauki tsawon shekaru kimanin uku ana gudanar da wanann aiki, wanda kuma yake samun karbuwa daga kasashen da ake yi ma aiki.
Daga cikin ayyukan da cibiyar ke yi har da gina masallatai da kuma makarantu na addini, domin koyar da yara karatu da rubutua cikin kasashe masu bukata.