IQNA

Mika Tsaron Haramomi Biyu Masu Tsarki Ga Sojojin Pakistan

23:42 - July 20, 2016
Lambar Labari: 3480629
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar saudiyya ta mika nauyin tsaron haramomi biyu masu tsarki ga runduna r sojin kasar Pakistan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yadsa labarai na yanar gizo na jaridar Khaibar cewa, bisa wasu bayanai masu tabbaci da aka samu daga majiyoyin gwamnatin Pakistan, a ziyarar da Rahil Sharif bababn hafsan hafsoshin kasar Pakistan ya kai kasar saudiyya a ‘yan kwanakin baya ya gana da sarki masarautar Saudiyya, kuma a lokacin suka suka cimma matsaya kan hakan.

Bisa ga yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin mahukuntan na Saudiyya da bangaren Pakistan, jami’an tsaron Sadiyya za su kula da tsaron haramomin guda biyu masu tsarki da ke Makka da Madina daga cikin gininsu da kuma harabarsu, yayin da sojojin Pakistan za su kula da tsaronsu daga waje da kuma saran hanyoyi da ke isa gare su daga cikin gari.

Wannan ya nuna yadda mahukuntan na Saudiyya suke fargabar kada a sake maiamita abin da abin da ya faru na kisan alhazai a shekarar da ta gabata, a lokacin da suka kullewa alhazai hanyar isa wurin jamra, inda dubbai suka rasa rayukansu, wanda hakan ya zubar da mutncin mahukunatn kasa a a idon duniya, sakamakon sakaci da rayukan masu gudanar da aikin hajji bakin ubangiji.

3516644

captcha