IQNA

Kai Hari A Fghanistan / Daesh Ta Dauki Nauyi

23:54 - July 24, 2016
Lambar Labari: 3480643
Bangaren kasa da kasa, al'ummar kasar Afghanistan na zaman makoki a ranar Lahadi bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai birnin Kabul ranar Asabar da ya yi sanadiyyar mutuwar sama damutane tamanin.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga Press TV cewa, fiye da mutane tamanin suka rasu wasu kimanin 170 kuma sukasamu raunuka a harin da aka kai cikin masu zanga-zanga 'yan kabilar Hazara marasa rinjaye, wadanda galibin su 'yan shi'a ne.

Shugaba Ashraf Ghani ya ce ya yi matukar bakin ciki da harin, inda ya sha alwashin daukar fansar mutanen da aka hallaka.

Ofishin MDD a Afghanistan ya bayyana harin a matsayin laifin yaki.

Kungiyar Daesh ta ce ita ce ta kai harin.

Kungiyar 'yan ta'ada ta Daesh ta dau alhakin kai wani mumunan hari da ya yi sanadin rasuwar mutane kimanin tamanin da raunana wasu a kalla dari biyu a birnin Kabul na kasar Afganistan.

A bangare guda, zabihullahi mujahid kakakin kungiyar taliban ya sanar da cewa manbobin kungiyar su ne suka kai hari a guraren jami'an tsaron arabkiyan masu goyon bayan Gwamnatin gani a yankin Aklaq na kauyen Derzab dake cikin jihar Jorjan inda suka halaka tare da jikkata uku daga cikin su.

Wata sanarwa da kungiyar ta wallafa a shafin ta na yada labarai ta ce wasu mayakan ta ne biyu suka kaddamar da harin.

bayanai da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar sun nuna cewa mutane uku suka shirya kai hare-haren, kuma daya ne daga cikin su ya samu ya tarwatsa kansa.

Anyi nasara hallaka dayan kafin ya tarwatshe yayin da na biyu boma-boman sa suka rusa dashi kansa.

An dai kai harin ne a daidai lokacin 'yan kabilar Hazara mabiya bazahabar shi'a ke jerin gwanolumana a birnin na Kabul domin yin allawadai da kyammar da aka nuna masu.

Wasu bayanai na daban sun ce akwai yiwuwar adadin mutanen da suka rasuya karu.

3517144

captcha