IQNA

Zaman Kusanto Da Fahimta Tsakanin Shi’a Da Sunnah A Masar

23:28 - August 08, 2016
Lambar Labari: 3480689
Bangaren kasa da kasa, Ahmad Karima daya daga cikin manyan malaman fikihu na cibiyar Azahar ya bayyana cewa za a gudanar da zaman kusanto da fahimta tsakanin shi’a da sunnah.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Yaum Sabi cewa, Ahmad Karima ya bayyana cewa wannan taro zai gudana ne karshen wannan wata na miladiyya tare da halartar wasu daga cikin manyan malaman cibiyar Azahar da kuam wasu masana na kasar Masar.

Ya ce taron zai samu halartar ‘yan kasar ta Masar ne kawai da suka hada da malamai da kuma masana daga bangarorin biyu na sunna da shi’a a matsayin mataklin farko, tare da fatan haka ya ci gaba ta yadda a nan gaba zai kunshi har da malamai da masana daga kasashen duniya.

Malamin ya kara da cewa babbar manufar gudanar da wannan taro dai ita ce kusanto da fahimta a tskanin wadannan muhimamn bangarori biyu na addinin musulunci, kamar yadda kuma a taron za a tattauna wasu batutuwan na daban, da hakan zai hada har da tatatunawa tsakanin musulmi da mabiya addinin kirista.

3520965

captcha