IQNA

Daurin Shekaru 5 Kan Wani Dan Algeria Da Ya Juya Kur’ani

22:02 - August 14, 2016
Lambar Labari: 3480709
Bangaren kasa da kasa, wata kotun kasar Algeria ta yanke hukuncin daurin shekaru 5 a kan wani dan kasar da ya keta alfarmar kur’ani.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Al-shuruq cewa, wata kotun a yankin Bani Warsilan a lardin Satif a kasar Algeria ta yanke hukuncin daurin shekaru 5 a kan wani dan kasar da ake kira B.S wanda ya keta alfarmar kur’ani da cin zarafin manzo (SAW)

Mutmin dai da ya kasance musulmi, amma daga bisani kuma ya karbi addinin kiristanci.

Hakan na kuma a halin yanzu yan ada sheka46 da haihuwa a duniya, kma mafi yawan lokacinsa yana karar da shi ne a kan yanar gizo da shaiga shafukan zmunta, inda anan ya zama kirista.

Daga cikin abubuwan da yake yadawa ashafukan yanar gioz a halin yanzu har da saka shakku kan kur’ani da kuma cin zarafin amnzo (SAW) da kuma jingina karya da aibanta matansa.

An dai kame shi ne a lokacin da yake shiorin yin wata tafiya acikin kasar ta Algeriya, wada kuma ahalin yanzu zai ci gaba da zama a gidan kaso bayan yanke wannan hukunci.

3522548

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kasa da kasa algeria
captcha