IQNA

Shugaban Tawagar Alhazai Ta Senegal:

Iran Tana Hidima Ne Ga 'Yan Adamtaka Ba Ga Musulunci Kadai Ba

23:38 - August 21, 2016
Lambar Labari: 3480730
Bangaren kasa da kasa, Abdulaziz Kabeh shugaban tawagar alahazan Senegala ganawarsa da shugaban ofishin al'adu na Iran ya bayyana cewa abin da Iran take yi hidima ce ga 'yan adam baki daya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na cibiyar yada al'adun muslunci cewa, tawagar alhazan kasar Senegal karkashin jagorancin Abdulaziz Kabeh ta gana da shugaban ofishin yada al'adu an Iran a Senegal Sayyid Hassan Ismati.

Wannan ganawa dai ta tabo muhimman batutuwa da suka shafi koyarwar addini wadda ta hada dukkanin bangarorin musulmi, musamman kuma kasashen Senegal da Iran kasashe ad suke da alaka mai karfi ta fuskar al'adu da kuma alaka da muslunci tun tsawon shekaru.

Shugaban hukumar alahazan kasar ta Senegal ya bayyana cewa suna jin dadin irin rawar da kasar Iran take takawa a dukkanin bangarori an siyasar kasashen muslmi, inda takan yi tsayin daka wajen ganin ta kare manufofin muslumi maimakon mika wuya ga masu kiyayya da muslunci.

Kamar yadda y ace kasar ta Iran tana gudanar da ayyuka wadanda ba domin wadanda take taimaka ma wa musulmi ne ba, sai domin jin kai irin na addinin muslunci, wanda kuma hakan shi ne babban abin da ake bukata ahalin yanzu, domin sauran al'ummomi su gane cewa muuslmi ba makiyi ba ne.

Daga karshe yay aba da kyautuka da aka ba su, inda kuma yayi addu'a ga manyan mutane da suka shahada a tafarkin juyin Islama irin su Shahid Beheshti da kuma Bahonar da sauransu.

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna senegal
captcha