Bangaren kasa da kasa, mata musulmi a kasar Amurka a cikin wani fim mai suna lemar Allah da aka watsa a yanar gizo sun bayyana dalilinsu na saka hijabi.
Kamfanin
dillanicn labaran kur’ani na Iqna ya habarta cewa, cibiyar Imam Ali (AS) ta
fitar da wani sabon fim na bidiyo a manhajarta ta telegram, wanda a cikinsa
mata musulmi na kasar Amurka a wata zantawa da jaridar Los Angeles Times, suke
bayyana dalilansu na zabar saka hijabin muslunci.