Kamfanin dillancin labaran kur'ani iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Christian Daily cewa, muuslmi da kiristoci sun gudanar da zaman ne a birnin Kaduna, daya daga cikin manyan biranan arewacin kasar.
Babbar manufar wannan cibiya dai it ace yada fahimtar juna da kauna a tsakanin jama’ar Najeriya, da kuma kauce wa duk wani abin da zai kawo tashin hankali a tsakanin jama’a, musamman ma dai mabiya wadannan manyan addnai na kasar.
Fiye da mutane dubu 20 ne dai ake cewa sun mutu sakamakon tashe-tashen hankula a Najeriya a cikin shekarun baya-bayan nan, duk kuwa da cewa mahuknta bas u tabbatar da wannan dadadi ba.
Olaw Fiske babban sakataren majalisar majam’ion mabiya addinin mirista na duniya dangane da wannan batu ya bayyana cewa; hakika kafa wannan cibiya a Kaduna yana da matukar muhimmanci, kuma zai mayar da wannan birnin babbar cibiyar sulhu da zaman lafiya a kasar baki daya.