Kamfanin dillanicn lbaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na sultanah cewa, jiya Juma'a Kotun kolin kasar Faransa, ta raba gardama kan zazzafar mahawarar hana saka suturar Burkini ga mata Musulmi a kasar inda ta yi watsi da kudirin kananan hukomomi, na hana amfani da suturar mai rufe jiki ga mata musulmi a wuraren shakatawa na bakin ruwa.
A cewar kotun kolin dai ana iya amfani da irin wannan mataki na takaita yanci ne idan har sun fuskanci cewa akwai matsaloli da ka iya haifar da tarnaki ga tsaron lafiyar al'umma ne kawai .
Kudirin hana mata Musulmi suturta jikinsu da ya samu goyon bayan Prime Minister Manuel Valls, ya haifar da mahawara mai zafin gaske a kasar Faransa.faransawa mata musulmi da dama ne suka fuskanci tilasta masu tube suturar ta burkini da suke sanye da ita a gabobin ruwan kasar ta Fransa, daga jami’an ‘yan sanda.
Kungiyoyin musulmi a kasar dai sun yaba da wannan mataki da kotun kolin ta dauka.