Malamin ya ci gaba da cewa aikin hajji yana bukatar hakuri matuka, ta fskar gajiyar jiki, da bakunta, da wahalhalu da ke cikinsa, da kuma yadda mutum zai hadu da mutane da kasashen duniya da al’adu daban-daban.
Haka nan kuma ya yi ishara da abin da ya faru a shekarar da ta gabata, inda aka kasha alhazai dubbai lokacin gudanar da aikin hajji, lamarin da ya saka jama’a da dama yin shiri a lokacin tafiyarsu aikin hajjin bana, na wata kila su dawo, ko kuma basu dawo ba.
Najeriya dai na daga cikin kasashen da suka rasa alhazai da dama a lokacin aikin hajjin bara a lokacin jifar shedan a Mina, inda fiye da maniyantan kasar 270 suka riga mu gidan gaskiya.
Kamar yadda kuma limamin ya ja hankulan maniyyata da su tsarkake niyya ga Allah shi kadai a lokacin aikin hajji da sauran ayyuka na ibada, domin kuwa duk wanda ya yi wani aiki ba domin Allah ba, to bas hi da ladar wannan aikin a wajen Allah.
Dangane da guzuri kuma ya ja hankulan jama’a da su tabbatar da cewa sun guzuri ne da abin da yake daga halal, domin kuwa Allah madaukakin sarki mai tsarki ne baya karba sai mai tsarki.