IQNA

Mahukuntan Saudiyyah Sun Kame Ahazai 20 Na Bahrain

19:44 - September 13, 2016
Lambar Labari: 3480776
Bangaren kasa da kasa, mahukuntan kasar Saudyyah sun kam wasu alhazai kimanin 20 na kasar Bahrain kuma ba a san inda suka na da su ba.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na hashtagsyria.com cewa, Yusuf Rabi shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na Bahrain ya bayyana cewa, dukkanin ahazan kasar Bahrain da aka kame Sadyya an kame su ne a daidaiku, kuma har yanzu ba a san makomarsu ba.

Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin alhazan an kame su ne bisa hujjoji da ba asani ba, domin kuwa mahukuntan Bahrain da na Saudiyya bas u komai kan lamarin ba, amma dai hakan bay a rasa nasaba da batutuwa na siyasa.

Duk kuwa da cewa wasu majiyoyi a kasar Bahrain na cewa sun ji wasu majiyoyi a ma’aikatar kula da harkokin ahazai ta kasar na cewa an kame alhazan ne saboda rashin samun izinin shiga kasar saudiyya a hukumance.

Gwamnatocin kasashen biyu dai sun jima sna aiki tare domin tabbatar da cewa sn murkuhse dukkanin mutanen da sue adawa da gwamnatin kasar ta Bahrain a siyasance.

Kwamitin kare hakkin bil adama na kasa Bahrain ya danganta abin da rashin gaskiya, ganin cewa babu wani bayani takamaimai daga dukaknin bangarrn biyu, dlamain da ke nuni da cewa akwa wani hadin bai a tsaanins.

Kamar yadda kwamitin ya bukaci ma’aikatar kula da harkokin aahaza ta kasar da ta mika masa sunayen mutanen da ake tsare da su a hannun jami’an tsaron Saudiyya domin bin kadun lamarinsu.

3529993


captcha