IQNA

Magajin Garin Makka Ya Yi Babatu Kan Kisan Alhazan Bara

15:50 - September 15, 2016
Lambar Labari: 3480781
Bangaren kasa da kasa, magajin garin birnin Makka mai alfarma ya yi babatu dangane da kisan gangancin da aka yi wa alhazai a shekarar bara.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na jaridar jaridar Alhayat ta kasar Saudiyya cewa, Khalid Faisal magajin garin birnin Makka kuma shugaban kwamitin aikin hajji, ya bayyana cewa aikin hajjin bana ya karyata maganganun cewa ba su iya tafiyar da hajji.

Ya ce abin da ya faru a ana ya tabbatar da cewa kasarsa za ta iya daukar nauyin aikin hajji da kula da lafiya da kuma rayuwar alhazai baki daya, sabanin abin da wasu suke fada na cewa Saudiyya ta gaza a kwace tafiyar da aikin hajji daga hannunta a mayar da shi ga hannun kasashen muuslmi baki daya.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa Iran tana da damar da zata yi abin da take so a kasarta, amma ba za su bari Iran ta yi abin da take so a cikin Makka da Madina ba.

Magajin garin yana mai shara da cewa sun hana alhazan Iran zuwa hajji ne saboda Iran tana yin abin ya sabawa mahangarsu a aikin hajji, alhali bai yi ishara da hana alhazan kasashen Syria da Yemen zuwa hajji da Saudiyya ta yi a bana ba.

A shekarar da ta gabata ce dai aka kasha dubban alhazai a wajen aikin jifar sheda sakamakon sakaci daa mahukuntan masaratar yayan Saud.

3530359


captcha