Kafin wannan lokacin dai ya sanar da cewa ya karbi addinin musulunci bayan da ya gamsu da abin da ya fahimta daga koyarwar wannan addini mai tsarki.
Calis yay i godiya ga Fauziya Bakrwadda it ace ta fara daukar shi hoto tare da matarsa a cikin aikin hajji tare da yada shi a yanar gizo.
Simon Calis ya zama jakada a cikin kasashen ketare tun bayan da ma’aikatar harkokin wajen Birtaniya ta dauke shi aiki a shekara ta 1978 a kasashen Qatar, Iraki da kuma Syria.
Haka nan kuma ya zama jakada a Dubai da basara da New Delhi da Tunisia gami da Aman.