IQNA

A Karon Farko Ban I Moon Ya Caccaki Isra’ila

16:00 - September 16, 2016
Lambar Labari: 3480786
Bangaren kasa da kasa, sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki moon ya yi amfani da kakkausan lafazi ga firai ministan Isra'ila.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Indian Express cewa, a karon farko firayi babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya caccaki firayi ministan haramtacciyar kasar Isra'ila kan ci gaba da mamaye yankunan Palastinawa da kuma gina matsunan yahudawa da yake yi a cikinsu, inda ya ce wannan aikin zalunci ne wanda ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa,

Inda shi kuma ya bayyana duk mutumin da ke adawa da shirin kasarsa na fadada yankinta zuwa yankin Palasdinawa, da mai marawa kokarin kawar da wani jinsi daga ban kasa.

Mista Ban Ki-Moon ya bayyana kalaman fira ministan Isra’ila da cewa kalamai masu matukar sosa rai.

Ya kuma ce ya kamata ya sani cewa shirin fadada girman Isra'ila haramtacce ne.

Sai dai kuma wannan na zuwa ne watanni kadan kafin Mista Ban Ki-Moon ya bar ofis, a karshen wannan shekarar.

3530477


captcha