Farras Al-Ibrahimi shi ne babban darakta na wannan cibiya ya kuma bayyana cewa, yanzu haka dai aikin ya yi nisa, kuma zai zama shi ne irinsa na farko da wannna babbar madaba’anta da ke karkashin hubbare Abbas (AS) take aiwatarwa.
Ya ci gaba da cewa, babbar manufar wannan aiki dai ita ce yada addu’oi da aka gada da manzon Allah da kuma iyalan gidansa tsarkaka, da kuma sauran abubuwa da suka danganci ilimi na addinin muslunci, wanda kuma ana samun nasara wajen gudanar da aikin kamar yadda ya kamata.
Dangane da aikin bugun littafin ya ce akwai kwamiti na sanyan ido da kuma yin gyara, wadanda suke kula da dukkanin aiki tare da tabbatare da cewa aikin ya gudana kamar yadda aka tsara shi ba tare da wata matsala ba.
Bayan kammala bugun littafin na mafatihul jinan guda miliyan daya, za a rarraba shi a wurare masu tsarki da suka hada da masallatai da kuma hubbarori a ciki da wajen kasar ta Iraki.
Dukkanin akin buga wannan adadi mai yawa na wannan littafi dai cibiyar ta Kafil ce ta dauke nauyinsa, tare da taimakon hubbaren mai tsarki, kuma bugun ana yinsa bisa tsarin rubutu da Hamid Sa’adi.
Kamar yadda kuma dukkanin aiyyukan da ake na tsare-tsare daga hubbaren ne, da hakan ya hada da zane da kuma tsara ciki da wajen littafin da ake bugawa gami kawata shi.