IQNA

An Yi Jerin Gwanon Neman A Saki Sheikh Zakzaky A Najeriya

17:44 - September 18, 2016
Lambar Labari: 3480790
Mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya na ci gaba da zanga-zangar Lumana ta neman a saki Shekh Ibrahim Elzakzaky.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya barata cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na A jiya Juma'a Dariruwan mabiya mazhabar shi'a ne suka gudanar da zanga-zangar lumana domin goyon bayan su ga shekh Ibrahim Yakubu Elzakzaky Jagoran 'yan uwa musulmi a Najeriya tare da neman Gwamnatin ta gaggauta sakin sa.

Mahalarta zanga-zangar na dauke da kyalaye mai dauke da hoton Shekh Ibrahim Yakubu Elzakzaky Jagoran 'yan uwa musulmi a kasar tare da rera taken yin alawadai kan kisan killan da Sojojin Najeriya suka yi wa dariruwan 'yan uwansu.

A ranar sha uku ga watan disamba shekarar dubu biyu da sha biyar din da ta gabata ne Sojojin Najeriya cikin manyan tankoki da motoci yaki suka kai farmaki Husainiya Bakiyatulla da kuma gidan Shekh Ibrahim Yakubu Elzakzaky jagoran 'yan uwa musulmi mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya inda suka kashe 'ya'yansa da dariruwan mabiyan sa daga cikin su a kwai mata da kananen yara.sannan kuma suka kame Shekh din tare da mai dakinsa bayan da suka ji musu munanan raunuka ta hanyar halbinsu da bindiga a wurare daban-daban na sashen jikinsu.

Wata majiya na cewa Shekh Ibrahim Elzakzaky na cikin mawuyacin yanayi na rashin Lafiya inda ake ce Idansa guda ba ya gani a halin da ake ciki wanda haka ne ma ya sanya Lauyoyin sa suka bukaci da a bada belinsa domin yi masa magani to saidai Gwamnatin Najeriya ta yi burus da wannan bukata.

3530883


An Yi Jerin Gwanon Neman A Saki Sheikh Zakzaky A Najeriya

captcha