Ya ce tun kafin wannan lokaci wata kotu ta bukaci hakan, amma an daukaka kara inda kotun daukaka kara ta ce hana saka hijabi ga mata dalibai tauye hakokins ne na addini.
Babban abin da masu wannan kumaji suke fakewa da shi dai shi ne batun ta’addanci, wanda jahar Lagos ba ta daga cikin jahohin da suke fusantar wannan matsala, kuma hatta inda ke da matsalar ta ragu matuka a halin yanzu.
Wannan martini yazo ne a lokacin da wasu suka dage tare da nuna rashin amincewa da matakin da kotun daukaka kara ta dauka, inda suke neman su kai maganar zuwa wata kotun ta daban domin tabbatar da cewa an hana daliban musulmi saka hijabi a fadin jahar ta Lagos.
Ga dukkanin alamu dai ko a wannan karo lamarin ba zai wani tasiri o nasara ba, domin kuwa mafi yawan jama’ar jahar wadanda musulmi ne ba su amince da hakan ba, kuma a shirye suke su fuskanci duk wanda zai tilasta matansu a jiye hijabi.