IQNA

Jerin Gwanon Neman A Saki Sheikh Zakzaky A Najeriya

13:49 - September 25, 2016
Lambar Labari: 3480803
Bangaren kasa da kasa, 'Yan Uwa musulmi a Najeriya na ci gaba da zanga-zangar lumana ta neman a saki shekh Ibrahim Yakubu Elzakzaky.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga press TV cewa dubun dubutan Al'ummar musulmi mabiya mazhabar shi'a almajiran shekh Elzakzaky ne suka gudanar da zanga- zangar Lumana na neman a saki jagoransu da mai dakinsa gami da sauren 'yan uwansu da ake tsare da su a gidan yari ba a kan ka'ida ba.

Zanga-zangar ta gudana a birnin Abuja jiya Alkhamis inda dubun dubutan mabiyan kungiyar ta 'yan uwa musulmi suka tattaru a birnin, saidai a yayin zanga-zangar jami'ar 'yan sanda sun watsa musu hayaki mai sanya hawaye domin tarwatsa su, sannan kuma sun kama wasu daga cikin mahalarta zanga-zangar.

Mahalarta zanga-zangar na bukatar da saki shekh Ibrahim Yakubu Elzakzaky ba tare da wani shardi ba sannan kuma a dakatar da irin cin zarafin da Dakarun tsaron Najeriya ke yiwa mabiya mazhabar shi'a a kasar.

Wannan zanga-zangar na zuwa ne a yayin da kungiyoyin kare hakin bil-adama ke ci gaba da bayyana fargabarsu kan halin rashin lafiya da Shekh din ke ciki.

Kungiyar "Yan'uwa Musulmi a Najeriya ta gudanar da Zanga-zangar neman a saki Sheik Ibrahim Zakzaky a birnin Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarun Rasa ya ambato cewa; Daruruwan 'yan kungiyar ta "Harkar Musulunci A Najeriya ne su ka yi zanga-zangar a birnin Abuja tare da neman a saki Sheikh Ibrahim alzakzaky ba tare da wani sharadi ba.

A bayanin da masu Zanga-zangar su ka fitar sun yi tir da kisan da sojojin su ka yi a Zaria tare kuma da yin kira a kawo karshen yadda ake cutar da 'yan shi'ar kasar.

Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma kulake wajen tarwatsa zanga-zangar ta lumana, kamar kuma yadda su ka kama wasu.

A Ranar 12 zuwa 14 ga watan Dicemba shekarar da ta gabata ce Sojojin Najeriya cikin tankoki da manyan motocin yaki suka kai farmaki kan Husainiya bakiyatull.. da gidan Shekh Ibrahim Yakubu Elzakzaky dake garin zariya inda suka yi kisan killa kan dariruwan 'yan uwa daga cikin su har mata da yara kanana.Sojojin Najeriyan sun aikata wannan aika-aika ne saboda an tarewa Shugaban Sojin kasa Laftanar Janar Yusuf Buratai.hanya.

Suhaila Zakzaky diyar sheikh Ibrahim Zakzaky ta bayyana cewa mahaofinta yana cikin wani yanayi mai mahala matuka, kasantuwar tun bayan harbinsa da bindiga ma sojoji suka yi, har yanzu bai samu kyakyawar kulawa da za ta ba shi damar murmurewa ba, mamakon hakan ma jikinsa yana ta tabarbarewa, musamman ma idonsa guda wanda aka harba da bindiga.

3532238


captcha