IQNA

Sallar Juma’a Tsakanin Sunna Da Shi’a A Lakhanu India

11:57 - September 26, 2016
Lambar Labari: 3480807
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wata sallar hadin kai tsakanin sunnah da shi’a a birnin Lakhanu na kasar India tare da halartar Sayyid Mahdi Alizadeh Musawi.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Times India cewa, a ranar Juma’a a masallacin Muhammad Shah a garin Lakhanu mai tarihi.

Bayanin ya ci gaba da cewa duk da cewa wannan birnin mabiya mazhabar suna ne ke tafiyar da shi, amma tare da halartar Sayyid Mahdi Alizadeh Musawi da Kab Sadeq shugaban kwamitin malamai na birnin da kuma wasu daga cikin ‘yan shi’a da sunna an gudanar da sallar ta bai daya.

Bayan kammala sallar Sayyid Mahdi Alizadeh Musawi ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana muhimmancin da ke tattare da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmi, musamman ma a wannan lokaci da makiya suka taso musulunci a gaba, a lokacin da su kuma musulmin suka rafkana.

Alizadeh ya ce babu wani banbanci tsakanin sunna da shi’a dukkaninsu musulmi ne, ko da kuwa akwai banbanci fahimta kan wasu abubuwa na gefe wadanda ba su ne asali ba, asali ne dais hi ne musunci da kalma shada wadda ta hada su.

3532390


captcha