IQNA

Babban Malamin Palastinu Ya Yi Allawadai Da Rufe Masallacin Ibrahimi

23:43 - October 04, 2016
Lambar Labari: 3480824
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Muhammad Hussain babban malami mai bayar da fatawa na Palastinu da Quds ya yi kakkausar suka dangane da yadda yahudawan sahyunya suka keta alfarmar haramin annabi Ibrahim a birnin Khalil.
Kafanin dillancin labaran kur’ani iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na gulfeyes cewa, sheikh Muhammad Hussain babban malami mai bayar da fatawa na Palastine bai daya ya bayyana matakin da yahudawa suka dauka na hana muuslmi salla a cikin masallacin annabi Ibrahim da cewa abin Allawadai ne.

Ya ce ko shakka babu wannan ba shi ne karon faro ba da yahudawan suka fara daukar wannan mataki ba, amma kuma a kowane lokaci abin da suke yi yana ta kara wuce haddi, a kan haka malamin ya yi kira da a taka wa yahudawan birki kan wannan tabargaza.

Sheikh Muhammad Hussain ya kara da cewa keta alfarmar wannan wuri mai tsarki keta alfarmar dukkanin addinai da Allah ya safkar daga sama ne, hatta a cikin addinin yahudanci yin hakan haramun ne.

A cikin wannan makon ne yahuadawan sahyuniya sanar da haramta wa duk wani musulmi shiga cikin haramin Ibrahimi da kuma wasu wanaki na musamman, da suka hada da ranakun 3, 4, 6, 12, 18 da kuma 19 na wannan wata na Oktoba.

Masallacin annabi Ibrahim dai yana da matsayi na biyu a cikin yankin Palastine a wajen al’ummar musulmi bayan masalacin aqsa mai alfarma.

3535403


captcha