IQNA

Sheikh Na'im Kasim: 'Yan Ta'addan Takfiriyyah Sun Bata Sunan Musulunci A Duniya

22:33 - October 08, 2016
Lambar Labari: 3480836
Bangaren kasa da kasa, mataimakin babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana 'yan ta'addan wahabiyyah Takfiriyyah a matsayin masu bata fuskar addinin muslunci a idon duniya.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Sheikh Na'im Kasim ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ta hada shi da jaridar Al-diyar ta kasar Lebanon wadda aka buga a yau Asabar, inda ya ce abin da 'yan ta'adda suke aikatawa da sunan addinin muslunci ba shi da wata alaka da muslunci, domin kuwa a cewarsa muslunci addinin rahma ne da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakaninsa da sauran addinai, jihadi na zuwa ne a matsayin mataki na kare kai.

Ya ci gaba da cewa matsayin da kungiyarsu ta dauka na fatattakar 'yan ta'adda a cikin Lebanon da ma wasu wurare da suke barazana ga al'umma tana nan daram a kansa, domin yakin da kungiyar ke yi da 'yan ta'adda tana yin hakan ne a madadin sauran al'umma.

Haka nan kuma malamin ya yi tir da Allawadai da yadda kasashen da suka kafa wadannan kungiyoyi na 'yan ta'adda suke ci gaba da daukar nauyinsu domin kawai a rusa a kasashen musulmi, inda ya ce kasashen Amurka, da wasu an turawa gami da Turkiya da kuma Saudiyyah, su ne kan gaba wajen daukar nauyin dukkanin ayyukan ta'addancin da kungiyoyi irin su ISIS da sauran su suke aikatawa a cikin Iraki da Syria.

Ya ce a kan haka yaki da ta'adanci yana bukatar hakuri da juriya, domin kuwa duk wanda yake yaki da wadannan kungiyoyi na 'yan ta'adda, yana yaki ne kai tsaye da kasashen da aka ambata.

3536342


captcha