A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin jihar Kaduna ya fitar, gwamnatin ta ce ta bada umurnin ne saboda yadda Malam Ibrahim Musa ya bayyana kan shi a matsayin dan kungiyar, bayan wasu sa'o'i da fara aiki da wata doka da ta haramta kungiyar ta 'yan Shi'a a jihar.
Bayan gwamnatin jihar ta sanar da haramta kungiyar ne, Ibrahim Musa, ya mayar da martani a madadin kungiyar, yana mai cewa za su kalubalanci matakin na gwamnati.
Sanarwar gwamnatin ta kuma bukaci dukkan hukumomin tsaro a jihar da su tabbatar da aiki da dokar da ta haramta kungiyar ta hanyar kama Ibrahim Musa.
Gwamnatin ta bayyana ikirarin da kakakin kungiyar ya yi a matsayin rashin mutunta umurninta, a don haka ta ce ba za ta bar wani ko wata kungiya suka karya doka ba.
Sai dai, Malam Ibrahim Musa ya shaida cewa ba zai gabatar da kanshi ga hukumomi ba kamar yadda gwamnatin ta bukata, kamar yadda kuma bai yi mamaki da umurnin kama shin ba, sannan ya yi Allah wadai da shi.
Malam Ibrahim Musa ya ce ya mika batun ga lauyoyin shi, domin su yi nazari a kanshi domin fuskantar lamarin ta fuskar doka.
Ya kuma ce a ranar Lahadi, jami'an tsaro sun killace su lokacin da suke taron Ashura a Zaria, sannan an kama wasu 'yan uwansu goma sha biyar a birnin Kaduna, tare da harbin daya a kafa.
Kafin wanann lokacin da bisa ikirarin gwamnatin Kaduna, sojji sun bizne gawawwakin yan shi'a dari uku da arbain da takwas da suka kasha a rikicin Zaria, wanda kuma a halin yanzu gwamnatin ta Kaduna bata Magana kan hakan.