Ya shirya fina finai masu alaka da imani da ubangiji wanda aka nuna daya daga cikinsu a ranar 3 ga watan firilun shekara ta 2016.
Ya zuwa yanzu dai an nuna kasha 6 daga cikin fina-finan da suka kunshi btun ma’anar rayuwa bayan mutuwa, da shedan gami da iko da kuma muujiza.
Halartar Freeman a wannan husainiyya da ake gudanar da taron Ashura a Landan na ci gaba da samun ra’ayoyi daban-daban a shafukan yanar gizo.
Morgan Freeman ya samu kautuka na oska hr sau hudu, a cikin shekarar 2005 ya samu kyautar fin din yariya miloniya.
Haka nan kuma a cikin shekara ta 2012 ya samu kyauta da aka ba shi ta fim din golden club, wadda a cikin ya taka rawar direban Dizi wanda kuma ya samu yabo a kansa.