A bangare guda Majiyar tsaron kasar ta sanar da cewa Jiragen yakin saman kasar sun kai hari a wuraren 'yan ta'addar IS dake yammacin garin Ramadi na jihar Anbar, lamarin da ya yi sanadiyar hallaka 'yan ta'adda 13 tare da lalata wasu daga cikin motocin su.
Wannan hari na zuwa ne a yayin da 'yan ta'addar ke kokarin kai wa Sojojin Irakin hari a kan hanyar su ta garin Biji zuwa Hadisa, lamarin da ya yi sanadiyar dakile ta'addancin.
A gefe guda Rundunar hadin gwiwar da aka kafa don 'yanto garin Mosil ta sanar da fara kai hare- hare kan 'yan ta'addar a birnin na Mosil.
Hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da dakarun kasar Iraki suke shirin fara kaddamar da harin kwato birnin na Mausil daga ‘yan ta’addan takfiriyyah, lamarin ya harzuka kasashen da suke daukar nauyin ‘yan ta’addan.