IQNA

Matakin gwamnatin Jahar Kaduna 'yan Uwa Musulmi

22:50 - October 18, 2016
Lambar Labari: 3480862
Bangaren kasa da kasa, Samaila Muhamamd Mara na Kebbi ya nuna damuwa kan halin da aka jefa yan uwa musulmi a Najeriya tare da bayyana hakan a matsayin zalunci.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Daily Trust cewa, mahukuntan jahar Kaduna sun wanke kansu kan kisan yan shi'a da aka yi bayan da suka fara kai musu hari a ranar Ashura, inda yan isakan gari da zauna gari banz suka karbi jami'an tsaron suka ci gaba da yin abin da suke.

Harkar ta fitar da bayani da ke cewa, Gwamnati ta yi ta kokarin nuna dirar mikiyar da ta yi mana a matsayin fada tsakanin Harkar Musulunci da jama'ar gari. Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El Rufa'i ya nuna haka tun farkon ta'addancin a watan Disamba, a jawabinsa ga jama'ar jihar.

Maganganunsa da kuma yanayin fuskarsa tun a wancan lokacin ba su bar kowa a duhu ba, irin zaluncinsa da dagawarsa a kan 'yan uwa na Harkar Musulunci, ta hanyar amfani da dukkan jami'an gwamnati iyakar iyawarsa, ta boye da kuma bayyane.

Kuma mafi yawancin lokuta ma babu hujja, hankali da kuma kiyaye doka, yana nuna tsananin kiyayyarsa akan Harkar Musulunci.

A matsayinsa na wanda ya zalunce mu kwanan nan, ya sanya wata dokar zartarwa ta hana mu 'yancin da muke da shi na yin addini, tare da barazanar daurin shekaru 7 a gidan yari ga duk wanda aka kama yana aikatawa.

Don an bayyana cewa dokar da ya sanya karara ta sabawa duk wata dokar jihar da kasa baki daya; sai kuma ya sanya wai a kama tare da hukunta Malam Ibrahim Musa, Shugaban Dandalin yada labarai na Harkar Musulunci.

Ta ya kuma yanzu El Rufa'i zai yi kukan munafurci bayan ya sanya an aikata rashin adalci a kan wasu mutane saboda kiyayyayyarsa da ayyukansa a kan su.

'Yan iskan gari sun karanci manufar gwamnatin ne sai kuma suka aikata abin da suka aikata, tare da goyon baya dari bisa dari na dukkan jami'an tsaron da yake iko a kan su.

3538667


captcha