IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun kai Farmaki Kan makabartar Annabi Yusuf (AS)

22:19 - October 20, 2016
Lambar Labari: 3480867
Bangaren kasa da kasa, daruruwan yahudawan sahyuniya sun kai farmaki kan makabartar annabi a Yusuf (AS) da ke palastine.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Quds Alarabi cewa, yahudawan sun kai farmaki kan hubbaren annabi Yusuf (AS) da ke gabacin birnin Nablus.

A lokacin da yahudawan suke kan hanyarsu ta isa wurin, wasu daga cikin palastinawa sun nemi su tare hanyarsu, inda suka jikkata su.

Yahudawan sun yi amfani da bindigogi da makamai da ke hannusu a kan palastinawa, da hakan ya hada da harsasan roba, kamar yadda suke samun kariya daga jami'an tsaron haramtacciyar kasar Isra'ila a wannan tabargaza da suke aikatawa.

Makabartar annabi Yusuf (AS) dai tana gabashin birnin Nabllus da ke gabar yadda da kogin Jordan, kuma wannan bas hi ne karon farko da yahudawa masu tsatsauran raayi ke kai farmaki a wurin ba, inda keta alfarmar wannan wuri mai daraja, da ke dauke da kabarin annabin Allah mai madaukakin matsayi.

3539404


captcha