IQNA

An Kafa Kwamitin Sa Ido Kan Makarantun Kur'ani A Algeria

9:50 - October 28, 2016
Lambar Labari: 3480884
Bangraen kasa da kasa, an kafa wani kwamitin sa ido kan makarantun kur'ani a kasar Algeria.
An KafaKwamitinSaIdoKanMakarantunKur'ani A Algeria

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo jaridar Albilad cewa, ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Algeria ta kafa wani kwamiti wanda zai rika sanya ido kan dukkanin ayyukan da ake gudanarwa a makarantun kur'ani a kasar.

Babbar manufar wannan kwamiti dai sanya ido kan yadda ake koyar da karatu da kuma abubuwan da ake koyarwar, da yadda ake koyar da su, domin sanin abin da ake yi ya daidai ko kuwa ya sabawa kaida.

An dauki wannan mataki sakamakon yadda ake samun wasu daga cikin masu makarantu da suke koyar da akidar tsatsauran ra'ayi, wanda hakan kan sanya matasa shiga ayyuka na ta'addanci da sunan addini, saboda mummunar fahimtar da suka yi ma kur'ani mai tsarki.

Nuraddin Muhammad shi ne mataimakin babban darakta mai kula da harkokin da suka shafi kur'ani a ma'aikatar kula da harkokin addini, ya bayyana cewa wannan matakin shi ne yafi dacewa domin sanin abin da yake gudana a makarantun kur'ani na kasar.

Haka nan kuma ya yi ishara da wasu makarantun na gargajiya da suke bin tsohon tsarin koyar da karatun kur'ani da salon a da, wanda hakan yake bukatar a sanya ido tare da yin gyara, ta yadda za a samu ci gaba na zamani a wannan fuska.

Ya ce akwai wasu iyayen yara wadanda suka yi ta yin korafi ga hukuma, kan yadda yadda ake juya tuanin yaransu a makarantun kur'ani, inda suke zama masu tsatsauran ra'ayi fiye da kima.

3540638

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna algeria
captcha