IQNA

Ma’aikatar Addinai A Masar: Salafawa Ba Su Da Hakkin Sukar Hudubobin Juma’a

21:30 - October 29, 2016
Lambar Labari: 3480886
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar ta sanar da cewa, salafawa ba su da hakkin sukar lamirin hudubobin Juma’a.
Kamfanin dlillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na kwamitin kula da harkokin addini a majalisar dokokin kasar Masar cewa, yan salafiyya ba su da hurumin da za su rika sukar hudubobin juma’a da ake gudanarwa a sauran masalatan kasar da ba na yan salafiyya ba.

Bayann kwamitin wanda ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta amince da shi ya ce, cibiyar Azahar ce kawai take da hakkin ta nada malamai da suka dace su zama limaman manyan masallatai da za su rika yin huduba.

Sheikh Bakar Abdulhadi babban daraktan ma’aikatar kula da harkokin addini a lardin Dumyat ya bayyana cewa, akwai horo na musamman da cibiyar Azhar take bayarwa ga malamai, wanda ta akan ne ake bayar da izinin zama limamai masu huduba, ba kungiyar salafiyya ce take da hakkin yin haka ba.

Dangane da laarin da aka yada kan cewa shi ne da kansa ya bayar da sanarwar cewa yan salafiyya suna hakkin huduba da zabar limamai da kuma wa’azia acikin masallatai, malamin ya bayyana cewa babu gaskiya a cikin wannan zancen, domin shi kansa bas hi da hakkin yin hakan.

3541484


captcha