Ya ce abin kunya ne ga masarautar 'ya'yan Saud su fake da birnin Makka mai alfarma ko dakin Ka'aba mai tsarki, domin neman goyon bayan musulmi kan ta'addancin da suke tafkawa kan fararen hula musulmi na kasar Yemen a kan idon al'ummomin duniya, domin a cewarsa babu wani abu da yake boye kan laifukan yaki da wannan masarauta take tafkawa a Yemen, inda ko a 'yan kwanakin nan ta kashe daruruwan mutane a wurin jana'iza a kan kamarori na 'yan jarida a birnin Sana'a, ban da dubbai da ta kashe a bisa alkalumman majalisar dinkin duniya da na kungiyoyin farar hula na duniya.
Ya ce a yau Yemen ta mayar da martani kan filin girgi na Jeddah da makami mai linzami, kuma ya samu wurin da aka saita daidai ba tare da wani kure ba, ya ce Makka da Madina wurare ne masu tsarki na dukkanin musulmin duniya, ba na 'ya'yan gidan Saud ba, kuma ba su taba kai musu hari ba kuma ba za su yi haka ba har abada.
Lukman ya kara da cewa, tunzura musulmi da karyar cewa an harba makami zuwa Makka, ba zai hana al'ummar Yemen ci gaba da mayar da martani kan muhimman biranan da ke karkashin ikon 'ya'yan gidan Saud ba, har sai sun daina kai hare-hare kan biranan Yemen, tare da daina kashe al'ummar kasar bisa zalunci da neman yin mulkin mallaka a kansu, domin a cewarsa ga dukkanin alamu duniya ta sanya ido ne har sai masautar 'ya'yan gidan saud ta karar da al'ummar Yemen baki daya.