IQNA

Sakamakon Izgili Sakataren Kungiyar Musulmi Ya Yi Ritaya

23:48 - November 01, 2016
Lambar Labari: 3480899
Bangaren kasa da kasa, Ayad Amin Madani babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya ajiye aikinsa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, sakamakon maganganu na rashin tunani da sanin ya kamata da Ayad Madani ya yi kan shugaban kasar Masar, ya fuskanci kakkausan martani daga Masar da ma kasashen dniya, wanda hakan yasa ala tilas a jiye aikinsa.

Ya daikasance daya daga cikin tsoffin ma’aikata a masarautar iyalan gidan saud,inda ya rike mukamai daban-daban da suka hada har da ministan hajji na kasar.

A daya bangare ministan harkokin wajen kasar Masar ya yi barazanar cewa kasarsa zata sake yin nazari kan alakarta da kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta O.I.C.

Wannan furuci na ministan harkokin wajen kasar Masar Shukri ya zo ne a yammacin jiya a matsayin mai da martani kan cin mutuncin da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta O.I.C Ayad Madani ya yi ne ga shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi.

Samaha Shukri ya kuma yi tofin Allah tsine kan matakin da Ayad Madani ya dauka na cin mutunci shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi tare da bayyana cin mutunci a matsayin muzanta babbar kasa irin Masar da ta kasance daya daga cikin kasashen da suka kafa kungiyar ta O.I.C.

A ranar Alhamis da ta gabata ce: Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta O.I.C Ayad Madani ya yi kuskuren kiran sunan shugaban kasar Tunusiya, inda ya kirashi da Abdul-Fatah Al-Sisi, sannan sai ya furta cewa yana da masaniyar babu komai a cikin firijin Abdul-Fatah Al-Sisi sai ruwa kadai.

Wannan furuci dai ya jawo tayar da jijiyoyn wuya atsakanin jami’an Masar da kuma kungiyar, inda daga karshe dai sakamakon izgili da yake fuskanta a kafofin yada labarai na kasashen larabawa daba-daban ya sanar da cewa ya ajiye aikin baki daya.

3542390


captcha