IQNA

21:19 - November 04, 2016
Lambar Labari: 3480906
Bangaren kasa da kasa, Gwamnan birnin Jakarta na kasar Indonesia na fuskantar gagarumar zanga-zanga daga dubban musulmi mazauna birnin, sakamakon wasu kalaman batunci kan kur'an mai tsarki da ake cewa magajin garin birnin ya yi.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin alghad.tv daga kasar Indonesia rahoton cewa, dubban musulmi sun fito a kan manyan titunan birnin jakarta suna gudanar da zanga-zangar yin Allawadai da kalaman da magajin garin birnin yayi, inda suke neman da ya safka daga kan mukaminsa.

Rahoton ce masu zanga-zangar sun tashi ne daga masallacin 'yanci daga cikin birnin jakarta bayan kammala sallar Juma'a, inda suka nufi fadar shugaban kasa domin kai kokensu na neman a safke magajin garin birnin, amma jami'an tsaroa  cikin kayan sarki sun hana su wucewa.

Bayanin ya ci gaba da cewa Basuki Tijahaja Pornama magajin garin birnin Jakarta, shi ne kirista na farko da ya taba zama magajin garin birnin Jakarta, wanda kuma dan asalin kasar China ne, inda ya bayyana cewa wasu daga cikin masu takara da shia  zaben da za a gudanar a shekara mai zuwa, suna yin amfani da ayoyin kur'ani mai tsarki suna yaudarar mutane domin su kada musu kuri'a, alhali a cewarsa wannan magana ce ta siyasa wadda ta doru a kan shirin da kake da shi ga jama'a idan suka zabe ka, ba magana ce ta addini ba.

Wannan furuci da magajin garin na Jakarta ya yi ya bata ma jama'a da dama rai, inda suke ganin ya tozarta kur'ani, wanda hakan ya sanya wasu dubbai suka shiga gudanar da zanga-zaga tare da neman a tsige shi tare da hukunta shi.

A yau an baza jami'an tsaro kimanin dubu 18 a bangarori daban-daban na nirnin Jakarta, domin tabbatar da cewa wani tashin hankali bai bai barke ba sakamakon hakan.

3543271Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، Jakarta ، Indonesia ، batunci ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: