IQNA

22:44 - November 05, 2016
Lambar Labari: 3480909
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila na shirin kafa dokar hana yin kiran asibahi a wasu yankuna da ke cikin birnin Qods.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na middle east monitoring cewa, wasu daga cikin yahdawan sahyuniya sun mika bukatar ganin an hana gudanar da kiran salla a masallatan palastinawa da ke kusa da matsugunnasu a cikin Quds da suka da Rahman, da tayyibah da kuma jami’ah da ke cikin unguwar Abu Dis.

A ‘yan kawanain da suka gabata ne Nir Barakat mai unguwar yankin ya bukaci ‘yan sanda da su dauki tsauraran matakai domin hana musulmi gudanar da kiran salla, domin acewarsa hakan yana damun yahudawa tare da hana su barci.

Bssam Bahr shi ne shuagabn kwamitin kula da harkokin palastinawa mazauna yankin Abu dis ya bayyana cewa, babu wani dalili da zai sanya daukar matakin hana yin kiran salla a masallatan musulmi da ke illa zalunci irin wanda suka saba gani daga gwamnatin yahudawan sahyuniya.

Ya ce masallatan da suke yankin suna cikin unguwannin palastinawa ne kawai, babu wani bafalastine da yake zaune a cikin matsugunnan yahudawa yan kaka gida, amma saboda neman fitina da tsokana suna neman a hana musulmi gudanar da ayyukansu na ibada.

Yanzu haka dai akwai matsugunnan yahudawa kimanin 15 da gwamnatin haratacciyar kasar Isra’ila ta gina a cikin wannan ynki na palastinawa da ta mamaye, inda yahudawa dubu 210 suke zaunea ciki, yayin da adadin palastinawan da ke yankin ya kai dubu 310.

3543498


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، Quds ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: