IQNA

23:51 - November 07, 2016
Lambar Labari: 3480918
Bnagaren kasa da kasa, babban kwamandan rundunar Furatul Ausat a Iraki ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun tanaji jami’an tsaro na musamman da za su yi aiki a taron arbain na imam Hussain (AS).

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanbar gizo na Fajr Muqawama cewa, Qis Muhammadawi babban kwamandan rundunar Furatul Ausat a Iraki ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun tanaji jami’an tsaro na musamman da za su yi aiki a taron arbain da suka hada har da masu aikin sa kai.

Muhammadawi ya ce ko shakka babu lamarin arba’in na wannan shekara na bukatar lura da kyau, bisa la’akari da yadda ‘yan ta’addan Daesh suke kokarin kwatar kansu, inda a yanzu suke kai hare-haren kan al’umma a cikin kasar.

Bisa la’akari da cewa miliyoyin mutane suke halartar wannan trao mai albarka na ziyarar arba’in na Imam Hussain (AS) hakan ya sanya sun tanaji jami’an tsaro na musamman da za su gudanar da ayyukan tsaro da bincike da sanya idoa taron, baya ga su kuma was dubai na sa kai da za su taimaka masu.

Ya ce ya zu yanzu an kafa wurare bincike a ciki da wajen birnin mai alfarma, kamar yadda kuma an fara karbar baki daga kasashen ketare da suke da niyyar halartar wannan babban taro mai albarka.

A banin nasa ya ce akwai mutane kimanin dubu 850 daga cikin Iraki da suka fara kama hanya domin halartar taron, kmar yadda kuma yanzu akan iyakokin Iran da Iraki akwai mutane kimanin dubu 25 da suke jiran a basu izinin shigowa kasar.

  1. 3544036


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، albarka ، bayyana cewa ، Imam Hussain ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: