IQNA

19:51 - November 08, 2016
Lambar Labari: 3480920
Bangaren kasa da kasa, wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari kan hubbaren annabi Yusuf (AS) da ke garin Nablus.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar na kamfanin dillancin labran ma'a na palastinu cewa, a yau da rana tsaka wasu mutane da ba a san ko su wane ne sun harba makaman roka a kan hubbaren annabi Yusuf (AS) mai alfarma.

Bayanin ya ce babu wani wanda aka kama, domin kuwa ana sa ran yahudawa masu tsatsauran ra'ayi ne suka kai wannan hari a kan wannan wuri mai tsarki, wanda kuma bas hi ne karon farko ba da suke kai samae a kan wurin tare da keta alfarmarsa.

Jami'an tsaron gwamnatin Palastinawa sun isa wurin tare da gudanar da bincike, domin tantance yadda lamarin ya wakana.

Yahudawan sahyuniya dai sun jima suna keta alfarmar wurare masu tsarki na msuulmi da suke cikin palastinu, da hakan ya hada har da msallacin Quds mai alfarma.

3544338


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: