IQNA

20:22 - November 09, 2016
Lambar Labari: 3480924
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar da dama suna nuna damuwa da fargaba kan zaben Donald Trump a matsayin shugaban kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Fortune cewa, musulmi a Amurka suna nuna damuwa kan zaben Trump sakamakon kalaman kin jinin muslunci da ya rika furtawa a baya.

Wani wanda sunansa Mukhtar ya bayyana cewa, baki bakaken fata suna cikin tsaka mai wuya.

Sai kuma wani mai suna Rwan, ya bayyana cewa ya damu matukan kan yadda mahaifinsa da mahaifiyarsa gami da ‘yan uwansa za su shiga, kasantur sub a yan asalin Amurka ba ne.

Da dama daga cikin musulmin da suka bayyana ra’ayoyinsu ashafukan sadarwa na Twitter suna cikin damuwa matuka, musamman ganin cewa Donald Trump mutum ne wanda ba ya boye maitarsa wajen nuna kiyayyarsa ga musulmi da kuma da kuma baki wadanda ba ‘yan asalin kasar Amurka.

Duk kuwa da cewa wasu na da ra’ayin cewa a ba shi lokaci domin ganin kamun ludayinsa, domin sau da yawa dan takara kan fadi maganganu domin burge su da ke da wani ra’ayi domin neman samun kuri’unsu, amma bayan lashe zabe, lamurra kan canja.

3544716


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: