Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya
nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anatoly cewa, wannan masallaci zai
dauki masallata dubu 4, kuma za a gina shi ne a fili mai fadin hekta 10, kamar
yadda kuma zai kunshi bangarori na al'adu da makaranta da kuma dakin karatu.
Masallacin za a gina shi ne da tsari irin na salon gine-ginen daukar usmaniya, kuma cibiyar kula da harkokin addini ta kasar Jibouti tana yin aiki tare da bangaren da ke gudanar da aikin.
Kasar Jibouti dai tana gabashin nahiyar Afirka ne, kuma kashi 99% na mutanen kasar musulmi ne masu bin mazhabar shafi'iyyah, kimanin mutane dubu 8 a kasar kuma suna bin mazhabar iyalan gidan manzo bisa kididdigar shekara ta 2009.
Kasantuwar kasar tana gefen ruwa, hakan ya bata damar samun damar yin hulda da kamfanonin kiragen ruwa na kasashen duniya da dama, inda a nan take samun kudaden shiga.
Babban birnin kasar shi ne Jibouti, kuma akwai mutane kimanin dubu 600 da suke rayuwa a cikinsa bisa kididdigar baya-bayan nan, haka nan kuma a sheakara ta 2008 ISESCO ta zabi birnin a matsayin birnin al'adun muslunci.