Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya
habarta cewa, ya nakalto daga shafin press TV cewa, A cikin wata sanarwa da
ma'aikatar cikin gidan kasar Spain din ta fitar a jiya Laraba ta ce 'yan sandan
kasar sun sami nsarar kame wasu mutane hudu, maza uku mace guda saboda zargin
janyo hankulan matasa da shigar da su kungiyoyin 'yan ta'adda irin su ISIS.
Sanarwar ta kara da cewa mutane hudun da aka kame din suna amfani da hanyar sadarwa ta internet ne wajen janyo hankulan matasan da shigar da su kungiyoyin 'yan ta'addan.
Tun daga shekara ta 2014 lokacin da kasar Spain ta sanya yanayin kasar cikin yanayi na halin ko ta kwana biyo bayan harin da aka kai birnin Paris na kasar Faransa, 'yan sandan kasar Spain din sun kame mutane 161 bisa zargin alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda.