IQNA

23:01 - November 11, 2016
Lambar Labari: 3480928
Bangaren kasa da kasa, an sake saka kalaman da zababben shugaban kasar Amurka yay i a na neman a hana musulmi shiga Amurka da kuma krarsu daga kasar a shafinsa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, babban dakaratan da ke kula da harkokin shafin yanar gizo na Donald Trump ya bayyana cewa, kalaman nasa sun zoa bayan kai wani da ka yi kan ofishinsa da ke cikin jahar California, wanda hakan ya harzuka shi, tare da yin wannan kira.

A lokacin da aka tambaye kan cewa bayan sanar da cewa Trump ya lashe zaben Amurka a cire wadannan kalamai, amma kuma an sake dawo da sua cikin shafin, sai ya bayyana cewa zai bincike kan lamarin.

A cikin watan Disamban shekarar 2015 da ta gabata ce, Trump ya bukaci da a hana musulmi shiga cikin kasar Amurka, tare da yin kira da a rika sanya ido a kan sauran musulmin da ke cikin kasar, tare da bincika masallatansu da wuraren ibadarsu.

3545024


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: