Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yada labarai na Express na kasar Birtaniya cewa, shahararren dan wasan damben ya saka hotunsa a cikin doguwar riga da hula wadda bisa ga al’ada musulmi ke saka irin wadannan kaya.
A lokacin da masu bin shafin nasa twitter suke tambayarsa kan dalilin yin haka sai ya bayyana cewa, a shekara ta 1964 Cassius Clay ya zama Muhammad Ali, yanzu kuma bayan shekaru hamsin Tyson Furu ya zama Riaz Tyson Muhammad.