Mutumin da ya sace kur’anin an kame shi ne bayan da wani mutum ya sanatr da ‘yan sanda abin da ya faru, a lokacin da wannan mutum ya dauki kur’anin daga cikin masallaci, bayan kame shi kuma ya amsa laifinsa.
Haka nan kuma na kame mtumin da ya sayi kur’anin daga hannun barawon, wanda ya sheda ma jami’an tsaro cewa shi ne ya sayi kur’anin, amma bai san cewa na sata ne ba.
Kotu ta yanke hukunci a kan mutumin da yay i satar na daurin shekara guda a gidan kaso, mai sayen kuma ya dauki alkawalin cewa ba zai sake sayen abin sata ba.
Kasar Sudan na daga cikin kasashen yankin da ake samun dadaddun kur’anai bugun hannu wadanda suke da kima idan za a sayar da su.