IQNA

Hanana Ta Zo Ta Uku A Gasar Kur’ani Ta Duniya

19:04 - November 17, 2016
Lambar Labari: 3480947
Bangaren kasa da kasa, a gasar kur’ani karatun kur’ani mai tsarki ta duniya ta mata zalla wadda ta wakilci Iran ta zo a matsayi na uku.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a cikin mutane 10 da suka fi nuna kwazo, Hanana Mustafa Khalafi 'yar shekaru tara da haihuwa ta zo a matsayi na uku a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta duniya kuma ta mata zalla, da aka kammala yau a brnin Dubai na UAE, tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashe saba’in da biyu na duniya.

Hanana Mustafa wadda ta wakilci kasar Iran, ita ce mafi karancin shekaru a sakanin daruruwan mahalarta gasar, wanda hakan ne ya sa tafi daukar hankulan kafofin yada labarai a gasar baki daya.

A gobe Juma'a ne za a gudanar da abar taron rufe gasar tare da halartar jami'ai daga kasar ta UAE dama wasu kasashen musulmi da na larabawa, tare da karrama wadanda suka fi nuna kwazo a gasar a cibiyar Sheikhah Fatima Bint Mubarak tare da halartar wakilan kasha fiye da 70 na duniya.

3546780


captcha