IQNA

23:53 - November 21, 2016
Lambar Labari: 3480960
Bangaren kasa da kasa, Abdullahi Ganduje gwamnan jahar Kano ya sanar da cewa mabiya mazhabar shi’a bas u da hakkin gudanar da wani taro sai sun samu izini daga jami’an tsaro.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na TV360 cewa, gwamnan jahar Kano ya hana mabiya mazhabar shi’a ‘yan jahar kano hudanar da dukkanin wani taro da ya shafe su, har sai sun samu izinin yin hakan daga jami’an tsaro.

Gwamnan ya ce ba za su bari ‘yan shi’a su rika taka doka ba, duk wani abin da ya shafe su da tarukansu ba za a sake gudanar da shi a cikin jahar ba, sai idan jami’an tsaro ne suka bayar da izini gare su.

Kamar yadda ya yi ishara da da abin da ya faru a ranar Litinin ta makon da ya gabata, inda mabiya mazhabar shi’a suka yi tattaki da nufin tafiya Zari’a, amma jami’an tsaro suka hana su, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 100 daga cikinsu.

Shekara guda kenan da kisan mutane fiye da dubu daya daga cikin ‘yan shi’a a garin Zaria, a lokacin da suke shirin gudanar da wani taron addini, kamar yadda kuma aka harbi jagoransu sheikh Ibrahim Zakzaky da harsasan bindiga, amma dai bai rasu ba, sai jami’an tsaro sun kame shi kuma har yanzu suna tsare da shi, ba tare da gurfanar da shi a gaban kuliya ba.

A kwanakin baya ma gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da haramta harkar muslunci ta mabiya mazhabar shi’a baki daya a fadin jahar, tare da shan alawashin shiga kafar wanda daya da mabiya harkar, bayan da gwamnan jahar ya ce haramta gudanar da dukkanin aikace-aikacensu jahar, bisa hujjar cewa ba su rijista ba.

3547518


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، Kaduna ، Kano ، Najeriya ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: