IQNA

Jagoran juyin Islama:

Kasashe Masu 'Yancin Siyasa Su Taka Rawa Wajen warware Rikicin gabas ta Tsakiya

22:48 - November 22, 2016
Lambar Labari: 3480962
Bangaren siyasa, jagoran juyin Islama na kasar Iran ya kirayi kasashe masu 'yancin siyasa da su safke nauyin da ya rataya kansu wajen ganin an kawo karshen zubara da jinin da ake a gabas ta tsakiya.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, Jagora juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, nauyi ne da ya rataya a kan Iran da ma sauran kasashe masu 'yancin siyasa, da su bayar da dukkanin gudunmawa domin ganin an samu zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yammacin yau Talata, a lokacin da yake ganawa da shugaban kasar Sloveniya Borut Pahor, wanda yake gudanar da ziyarar aiki a kasar Iran.

Jagoran ya kara da cewa, an kunna wutar rikici a yankin gabas ta tsakiya ne da nufin raunana kasashe masu 'yancin siyasa, tare da tabbatar da wanzuwar zalunci da mulkin mallaka a kan al'ummomin yankin, wanda kuma hakan tasirinsa ba zai tsaya kan al'ummomin da ake zalunta a yankin ba kawai, tasirinsa zai koma har zuwa ga wadanda suka kunna wutar rikicin tn daga farko.

Haka nan kuma jagoran ya yi ishara da karyar da Amurka da wasu 'yan kanzaginta suke yi na da'awar yaki da ta'addancin kungiyar ISIS, inda ya ce Amurka ba da gaske take yi kan yaki da ta'addanci ba, domin kuwa ita ce kan gaba wajen haifar da ta'addanci da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin gabas ta tsakiya, wanda kuma shi ne yake bazuwa zuwa sauran kasashe na duniya, kamar yadda hakan yake da babban tasiri wajen kwaraar dubban daruruwan 'yan gudun hijira zuwa turai daga kasashe masu fama da 'yan ta'adda.

Kamar yadda kuma ya yi ishara da zaluncin da al'ummar Yemen suke fuskanta dare da rana da kisan kiyashin da ake yi kansu da rusa musu kasa babu gaira babu sabar, sai domin neman yin mulkin mallaka a kansa tare da mayar da su bayi da karfin bindiga, kuma duniya tana kallo ta zura idanu.

A nasa bangaren shugaban kasar Slovenia Borut Pahor ya nuna jin dadinsa matuka dangane da ziyarar da yake gudanarwa a kasar ta Iran, tare da shan alwashin cewa yin aiki tare da kasar ta Iran a bangarori daban-daban, musamman ta fuskar kasuwanci da bunkasa harkokin tattalin arziki.

3548116


captcha