IQNA

22:51 - November 22, 2016
Lambar Labari: 3480963
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wata gasa ta kananan yara kan rubutun kur'ani mai tsarki a kasar Afirka ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren yada labarai na cibiyar yada ala'adun musulunci cewa, ofishin yada aladu na kasar Iran ne ya dauki nauyin shirya wannan gasa, mai taken WINTERVELD.

Bayanin ya ci gaba da cewa kanan yara musulmi ne suka samu halartar wannan gasa, inda suka rika yin zane na ayoyin kur'ani a wannan gasa, wanda ya zo daidai da ranar 20 ga watan Nuwamba wato ranar yara ta duniya, inda yara kimanin 100 suka shiga gasar.

An baya da wasu ayoyi da suke Magana kan batun rayuwar zamantakewa a cikin kur'ani domin rubuta su da kyakyawan rubutu.

Daga cikin ayoyin aya ta 31 daga surat A'araf, sai kuma 30 daga surat Anbiya, sai kuma 13 daga surat Hujurat, da ufin tantance kaifin basirar yaran da kuma yadda suke maida hankali ga rubutun kur'ani.

Babbar manufar gudanar da wannan gasar dai ita ce kara karfafa yaran musulmi kan koyon kur'ani mai tsarki da rubutunsa da kuma sanin ma'anonin ayoyinsa, tare da basu tarbiya kan koyarwar kur'ani mai tsarki, lamarin da ya samu karbuwa matuka daga musulmin kasar, kuma an bayar da kyutuka ga yara 10 da suka fi nuna kwazo.

3548005


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran kur’ani ، IQNA ، afirka ta kudu ، kasar ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: