IQNA

Iran Za Ta Yi Tare Da Kwalejin Addinin A Ethiopia

22:53 - November 28, 2016
Lambar Labari: 3480981
Bangaren kasa da kasa, Iran za ta yi aiki tare da kwalejin addinai ta mabiya addinin kirista na darikar Orthodox a kasar Ethiopia.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama'a a cibiyar yada al'adun muslunci cewa, Sayyid Hassan Haidari shugaban ofishin yada al'adun musulunci ya gana da Abuna Timotiyus cewa shugaban kwalejin addinai na Ethiopia.

Ya ce tattaunawar tasu ta mayar da hankali ne kan yadda za a samu taimakekeniya a tsakanin bangarorin biyu dangane da yin nazari kan addinai da kuma karawa juna sani, kuma sun cimma matsaya kan hakan.

Kasashen Iran da kuma Ethiopia dai suna da tsohon tarihi na dangantaka a dukkanin bangarori na al'adu da ilimi da ma kasuwanci, kasantuwar al'ummomin kasashen biyu suna da dadadden tushea tarihi na dubban shekaru.

Dukkanin bangarorin biyu dai sun amince a kan fara yin aiki dangane da yadda za su tsara hanyoyin karuwa da juna, inda Iran za ta rika tura masu bincike zuwa wannan kwaleji domin kara samun bayanai da kuma ilmomi da suka danganci akidun da ake koyarwa a wannan kwaleji.

A nata bangaren kuwa kwalejin za ta rika gudanar da bincike a cibiyoyin kaar Iran kan lamrinadini da kuma al'adu da suka danganci addinin muslunci.

3549266


captcha